IQNA

23:59 - August 01, 2018
Lambar Labari: 3482852
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan bindiga sun sace wasu ‘yan jarida hudu a kasar Libya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu masu dauke da makamai sun sace wasu ‘yan jarida 4 hudu a garin Tripoli na kasar Libya, wadanda suke aki da kamfanonin dillancin labarai na Reuters da kuma Faransa a kasar.

Bayanin ya ce wadannan ‘yan jarida su ne Hadi Amara da Ahmad Amami da suke aiki da reuters, sai kuma Mahmud da Hamza Turkiya da suke yin aiki da kamfanin dillancin labaran Faransa.

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasar Libya ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da sace wadannan ‘yan jarida da ‘yan bindiga suka yi, tare da yin kira da a sake su ba tare da wani bata lokaci ba.

Haka nan kuma kungiyar ta yi kira ga gwamnatin kasar ta Libya da ta dauki kwararan matakai na kae rayukan ‘yan jarida da suke gudanar da ayyukansu a kasar..

3735082

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، lokaci ، Libya ، jarida ، Tripoli
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: