Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na ciyar yada al’adun musulunci ya bayar da rahoton cewa, masallacin mabiya mazhabar shi’a a kasar Kenya zai dauki nauyin taron idin Ghadir khom da za a gudanar a mako mai zuwa.
Wannan taro dai zai samu halartar malamai da kuma masana daga bangarori daban-daban, daga ciki kuwa akwai wadanda za su gabatar da jawabi da kuma kasidu kan matsayin wannan rana, da kuma darussan da ke cikinta.
Bayan nan kuma za a gabatar da sallolin azuhura da la’asar a wurin kafin ci gaba da taron.