Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar radiyon RTL ta kasar Faransa ta bayar da rahoton cewa, a nazarin da wata babbar cibiyar bincike ta Pew Center da ke kasar Amurka ta yi, ta bayyana cewa bisa la'akari da karuwar musulmi a duniya, adadinsu zai kai biliyan 3 da doriya a cikin shekara ta 2060, idan aka yi la'akari da yawansu da ya kai biliyan 1.6 a cikin shekara ta 2010.
Cibiyar ta ce a halin yanzu mafi yawan musulmi suna zaune a yankunan tsakiyar Asia da kuma gabashinta da kuma kudanci, inda kashi 62 cikin dari na musulmin duniya suna a cikin wadannan yankunan ne.
Sauran musulmin kuma suna a cikin yankunan gabas ta tsakiya ne da arewacin Afirka, kamar yadda kuma sauran yankunan Afrika na bakaken bata za su zo a matsayi na uku, sai kuma sauran yankuna da suka hada da nahiyar turai, Amurka da kuma Latin, inda a dukkanin wadannan nahiyoyi adadin musulmi yana karuwa ne.
Sakamakon binciken cibiyar ya nuna cewa, baya ga hayayyafa da musulmi suke yi musamman kasashen ad suka fi yawa, a daya gefen kuma addinin muslucni shi ne addinin da ya fi saurin samun masu karbarsa fiye da dukkanin sauran addinai na duniya.