IQNA

Hardar Kur'ani Sharadin Zama Limami A Jordan

23:48 - September 03, 2018
Lambar Labari: 3482948
Bangaren kasa da kasa, an saka sharadin cewa dole ne mutum ya hardace kur'ani mai tsarki kafin zama limamin masallaci a Jordan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Jordan ta kafa sharadin na cewa dole ne malamai su hardace kur'ani mai tsarki kafin zama limamin masallaci a kasar.

Kamar yadda bayanin kuma ya yi ishara da cewa, idan hakan ba ta samu ba saboda wasu dalilai, to akalla malmi ya hardace rabin kur'ani.

Bayanin ya kara da cewa, daga lokacin da aka watsa wannan sanarwa a jiya, ta zama doka da za a yi aiki da ita a fadin kasar.

3743489

 

captcha