Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kutse cikin masallacin kudus ya fara zama jiki inda a kowane mako 'yanhudawa 'yan share wuri zaune su ke shiga cikinsa sau daya ko sau biyu.
a gefe daya sojojin sahayoniya sun kai hari a yankuna daban-daban na yammacin kogin Jordan, inda su ka yi awon gaba da palasdinawa sha biyar ba tare da tuhumarsu da wani laifi ba.
Bayan kamun mutane, an yi taho mu gama a tsakanin samarin palasdinawa da kuma sojojin 'yan sahayoniya.
Da a kwai Palasdinawa dubu shida da dari biyar a cikin kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila, dari uku daga cikinsu kananan yara.