Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Anatoly ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da UNICEF ta fitar, ta bayyana cewa kusan dukkanin kananan yara a kasar Yemen suna cikin hadarin mutuwa, sakamakon mummunan halin da suke ciki.
Bayanin na UNICEF ya kara da cewa, sakamakon hare-haren da jiragen yakin kawancen Saudiyya ke kaddamarwa a kan kasar ta Yemen, hakan ya yi sanadiyyar rushewar mafi yawan abubuwan da al’ummar kasar ke bukata domin rayuwa.
Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, a halin yanzu yunwa ita ce babbar barazana ga al’ummar kasar Yemen, musamman kananan yara, wadanda a halin yanzu suke mutuwa saboda rashin abinci, ga kuma kwalara saboda da sauran cututtuka masu hadari da suke lakume rayukan kananan yara.