IQNA

Wani Bafalastine Ya Yi Shahada 11 Kuma Sun Jikkata

23:43 - October 25, 2018
Lambar Labari: 3483075
Bangaren kasa da kasa, Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun harbe matashin ne a kusa da haramin annabi Ibrahim a tsakiyar garin al-khalil da ke kudancin kogin jOrdan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, sahayoniyar sun riya cewa matashin Bapalasdinan ya yi kokarin sarin wani soja ne da wuka.

Sau da yawa sojojin Sahayoniya suke harbe Palasdinawa suna masu riya cewa za su kai hari da wukake akan sojoji ko 'yan share wuri zauna.

Wani labarin daga Palasdinu ya ambaci cewa; Sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai hari akan Palasdinawa a mashigar Kalandiya.

A kowace rana ta Allah, 'yan sahayoniya suna kai hari ko kuma kama Palasdinawa a yankunan daban-daban na yammacin kogin Jordan.

3758453

 

captcha