IQNA

23:52 - November 01, 2018
Lambar Labari: 3483089
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da wani zaman taro mai taken sanin musulunci a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudanar da wani zaman taro mai taken sanin musulunci a kasar Canada a masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Admanto.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro yana a matsayin taron karawa juna sani ne, wanda zai tabo batutuwa masu matukar muhimmanci da suka shafi musulmi da kuma addinin muslunci.

Wasu daga cikin malamai za su gabatar da jawabi a wurin, inda za su amsa wasu daga cikin tambayoyin da wasu suke da su da su kan addinin muslunci, da suka hada da musulmin da ma wadanda ba musulmi ba.

Masallacin Imam Hussain (AS) dai na daga cikin muhimman cibiyoyin gudanar da taruka da suka shafi addinin muslunci a wannan birni, inda yak an karbi bakunci taruka daban-daban na musulmi, da suka hada da masu mabanbantan fahimta.

3760415

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: