IQNA

Ci Gaba Da Nuna Adawa Da Ziyarar Bin Salman A Tunisia

23:56 - November 26, 2018
Lambar Labari: 3483153
Lauyoyin kasar Tunisia sun mika bukatarsu ga kotun kasar kan ta dauki matakin hana yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman shiga cikin kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a ziyarar da yariman saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya fara a jiya, wadda ita ce ta farko tun bayan kisan Jamal Khashoggi a farkon watan Oktoba, ya fara da kasar UAE, inda kuma zai ziyarci wasu kasashen da suka hada da Bahrain, Masar, Aljeriya, Tunisia da kuma Mauritania, daga nan kuma zai wuce zuwa taron tattalin arziki a kasar Argentina.

Lauyoyin na kasar Tunisia sun bukaci kotun da ta dakatar da Ziyarar Muhammad Bin Salman a kasarsu ne, sakamakon zarginsa da ake yi da hannu kai tsaye a  kisan Jamal Khashoggi, da kuma yakin da yake kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen, inda ya zuwa yanzu ya kashe dubban kananan yara da mata a kasar ta Yemen da sauransu.

3767237

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha