
Kamfanin dillancin labaran iqna, ana ci gaba da zaman ta’aziyyar babban malamin addinin muslunci a kasar Uganda Sheikh Sauliti Kabuka wanda Allah yay i masa rasuwa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin kampala fadar mulkin kasar Uganda.
Malamin ya shahara wajen yin tarjamar kur’ani mai tsarki, da kuma tafsiri gami da karantarwa irin ta addinin mulsunci, inda yay aye dalibai masu tarin yawa musamman a bangaren kur’ani.
Dubban jama’a ne suke ci gaba da isa wurin taaziyarsa, da suka hada da malamai da’yan siyasa da jami’an gwamnati gami da malaman addinin kirista, wadanda suke bayyana shi a matsayin babban mutum mai karamci, wanda yake girmama jama’a muuslmi da kirista.