IQNA

Tun Farko Kasancewar Amurka A Syria Babban Kure Ne

23:43 - December 22, 2018
Lambar Labari: 3483240
Bahram Qasemi kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriya Musulinci ta Iran, ya bayyana hakan da cewa, tun farko dama kasancewar sojojin na Amurka a Siriyar kuskure ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a lokacin da yake sanar da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewa kasancewar dakarun na Amurka a yankin kure ne dama tun farko, sannan ba kan gaskia ne ba, hasali ma haddasa fitina ne.

Mista Qassemi, ya kara da cewa sanya kasar AMurka a yankin musamman a Siriya, hadassa rikici da matsalar rashin tsaro. 

A ranar Laraba data gabata ne shugaba Trump na Amurka ya sanar da janye sojojin kasarsa kimanin dubu biyu dake arewa maso gabashin Siriya wandanda ke dafawa mayakan kurdawa baya.

Kafofin yada labarai a Iran dai sun bayyana matakin na janye sojojin Amurka daga Siriya a matsayin babbar nasara ga Siriya, dama kawayenta Iran din da kuma Rasha dake goyan bayan gwamnatin Syria.

3774651

 

 

 

captcha