IQNA

An Buga Mujallar Kur'ani Ta Farko A Kasar Tunisia

23:32 - December 24, 2018
Lambar Labari: 3483248
A karon farko an buga wata mujalla ta kur'ani a kasar Tunisia, wadda kuma aka fara sayar da ita a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, tare da amincewar gwamnatin kasar Tunisia, a karon farko an buga wata mujalla ta kur'ani a kasar, wadda malamai da masana daga dukkanin sassan kasar za su rika fitar da bayanai da makaloli a cikinta tare da taimakon kasar Iran.

Fauzi Alawi wanda shi ne babban editan mujallar ya sheda wa manema labarai a jiya a birnin Tunis cewa, babbar manufar wannan mujalla ita ce ita ce fito da hakikanin koyarwar kur'ani mai tsarki ga al'umma, domin yada kyakyawar koyarwar irin ta kur'ani da kuma kalubalantar yada akidar ta'addanci a tsakanin musulmi ta hanyar yin amfani da ayoyin kur'ani mai tsarki.

Dukkanin malamai da masana da za su rika gabatar da makalolinsu da bayanansu a cikin mujallar fitattu ne  da suke da tasiri a kasar ta Tunisia, haka ann kuma za a rika buga mujallar domin sayar da ita  a kasuwa, da kuma wallafa ta a cikin shafukan yanar gizo, shirin da ake ganin zai yi babban tasiri musamman a tsakanin matasa na kasar.

Kasar Tunisia dai ita ce kasa ta biyu bayan Saudiyya, wajen yawan 'yan ta'adda da suke yaki a sahun kingiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Siriya da Iraki.

3774795

 

captcha