Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sojojin na Amurka sun fice daga Syria ne zuwa yankin Kurdestan na kasar Iraki, inda aka suka kafa wasu sansanoni da za su zauna a cikinsu.
Wannan mataki dai yana zuwa bayan sanarwar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayar ne a ranar goma sha tara ga watan Disamban da ya gabata, kan cewa sojojin Amurka za su fice daga kasar Syria, inda ya ce bai ga amfanin kasancewarsu a can ba.
A wani furucin da ya yi a ranar Laraba da ta gabata, Trump ya bayyana cewa babu abin da ke cikin Syria sai tarin yashi da kuma mutuwa, saboda haka babu wata ribar da Amurka za ta samu idan ta ci gaba da jibge sojojinta a kasar.
Wannan matakin dai ya sanya wasu daga cikin kasashen larabawa, daga cikinsu kuwa har da wadanda suka kwashe tsawon shekaru bakawai suna daukar nauyin 'yan ta'adda a Syria, sun fara sauya tunani, inda suke ganin shirwayawa da gwamnatin Syria a halin yanzu shi ne kawai mafita.