IQNA

Sudan: Sadiq Mahadi Ya Bukaci Shugaba Umar Hassan al-Bashir Ya Yi Murabus

14:34 - January 26, 2019
Lambar Labari: 3483328
Shugaban jam'iyyar Ummah, ta Sudan Sadiqul-Mahdi ya ce dole ne gwamnati ta yi murabus domin tsarin da take tafiya a kansa ba ya aiki

Sudan: Sadiq Mahadi Ya Bukaci Shugaba Umar Hassan al-Bashir Ya Yi MurabusSadiqul-Mahdi ya kuma kirayi magoya bayansa da su shiga cikin masu Zanga-zangar ruwan sanyi ta yin kira ga shugaba Umar Hassan al-Bashir da ya sauka daga kan mukaminsa

Bugu da kari shugaban na Jam'iyyar Ummah ya yi kira da a saki dukkanin fursunonin siyasa, sannan kuma ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an kashe mutanen da su ka kai 50

Tun ranar 19 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata ne al'ummar kasar Sudan su ka fara yin Zanga-zangar kin yarda da hauhawar farashin kayan masarufi. Sai da daga baya Zanga-zagar ta juye zuwa yin kira ga shugaban kasa Umar Hassan al-Bashir da ya yi murabus

Majiyar gwamnati ta ce adadin mutane da aka kashe a tsawon lokacin Zanga-zangar ba su wuce 29 ba, yayin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suke cewa an kashe mutane 40.

Wannan ce bijirewa mafi girma da mutanen kasar ta Sudan suke yi a tsawon shekarun mulkin Shugaba Umar Hassan al-Bashir wanda ya fara tun a 1993.

http://parstoday.com/ha/news/africa-i34955

captcha