IQNA

Jam’iyyar Labour A Birtaniya Ta Yi Watsi da Haramta Hizbullah

21:26 - February 27, 2019
Lambar Labari: 3483407
Bangaren kasa da kasa, a cikin wani bayani da ofishin jakadancin Lebanon A London ya fitar a yau, gwamnatin Lebanon ta nuna takaicinta kan kan matakin da Birtaniya ta dauka na haramta Hizbullah a kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, Jaridar Al-akhabr ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da da ofishin jakadancin na Lebanon a London ya fitar, gwamnatin Lebanon da al'ummar kasar ba su taba amincewa da duk wani mataki irin wannan akan kungiyar Hizbullah ba.

Bayanin ya ce kungiyar tana a matsayin wani bangare mai matukar muhimamnci a kasar Lebanon, kamar yadda take da wakilci a  cikin gwamnati, kuma take taka rawa a cikin dukkanin sauran lamurra da suka shafi al'ummar kasar.

A nata bangaren jam'iyyar Labour ta kasar Birtaniya ta yi kakkakusar suka kan wannan  mataki da gwamnatin kasar ta dauka, tare da shan alwashin cewa za ta kalubalanci hakan idan aka kai maganar a  gaban majalisar dokokin kasar.

 

3793795

 

 

 

 

 

 

captcha