IQNA

21:29 - February 27, 2019
Lambar Labari: 3483408
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron yahudawa sun kama gwamnan quds da wasu falastinawa 32 bayan bude kofar Babu-Rahama na massalacin Qudus mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto Cibiyar  dake kula da 'yan gidan kason Palastinawa na cewa a ci gaba da kame-kamen da jami'an tsaron sahayuna ke yi, a wannan Laraba sun kame Palastinawa 23 cikin kuwa harda gwamnan lardin Qudus da Mudhat Dabiyat lauya ta musaman kan birinin Qudus.

A yankunan Ramullah da Albirah  ma, jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ilan sun yi awan gaba da wasu Palastinawa da suka hada da Zakariya Zubaidi gungu a Majalisar juya hali na kungiyar 'yanto al'ummar Palastinu wato Fatah da Tariq Bargus wakili na kwamitin al'amuran da suka shafi 'yan gidan kaso da wadanda jami'an  tsaron sahayunan suka kame.

Daga makon da ya gabata zuwa yau larabawa, jami'an tsaron sahayunan sun kame Palastinawa sama da 100, wannan kuwa na zuwa ne bayan buda kofar babu-Rahama na massalacin Qudus mai tsarki.

A makon da ya gabata ne dariruwan Palastinawa suka fuskanci masallacin Qudus mai tsarki dake garin Qudus, inda suka bude kofofi shiga masallacin na Babu-Rahama 12, bayan rufe shi na tsahon 16 da hukumomin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi bisa da'awar tabbatar da tsaro.

3793912

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، tsaro ، quds
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: