IQNA

Sakamakon Jin Ra’ayi Jama’a A Amurka Ya Nuna Cewa Musulmi Ne Aka Tsana A Kasar

23:53 - March 09, 2019
Lambar Labari: 3483439
Bangaren kasa da kasa, wani saamakon jin ra’ayin jama’a a kasar Amurka ya nuna cewa musulmi su ne suka fi fuskantar tsangwama a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Yani Shafaq ta bayar da rahoton cewa, wasu manyan cibiyoyin bincike a kasar Amurka sun gudanar da jin ra’ayin jama’a, wanda saamakonsa ya nuna cewa musulmi su ne suka fi fuskantar tsangwama a kasar da kuma nuna musu wariya.

Bayanin ya ci gaba da cewa, cibiyoyin Harrisx da Hill ne suka gudanar da binciken an hadin gwiwa a dukkanin jahohin Amurka.

Kimanin kashi 85 cikin dari na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun nuna cewa musulmi ne suka fi fuskantar matsala da kuma nuna musu wariya saboda addininsu a kasar.

Da dama daga cikin cibiyoyin muuslmi a kasar Amurka sun bayyana cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, an samu matsaloli na cutar da musulmi fiye da sauran shekarun da suka gabata a kasar.

 

3796465

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha