IQNA

23:58 - April 16, 2019
Lambar Labari: 3483552

Isra’ila Na Tsare Da ‘Yan Jarida 22 A Gidajen Kaso

Bnagaren kasa da kasa, gwamnatin Ira’ila tana tsare da ‘yan jarida 22 gidan kaso bisa laifin dauka rahotanni a wuraren da jami’an tsaro suke kai farmaki kan Falastinawa.

Isra’ila Na Tsare Da ‘Yan Jarida 22 A Gidajen Kaso

Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, Cibiyar kula da kare hakkokin ‘yan jarida ta Falastinu ta fitar da wani bayani a jiya, wanda a cikinsa take bayyana cewa, a halin yanz akwai ‘yan jarida 22 a gidan kason Isra’ila da ake tsare da su 3 daga cikinsu mata ne.

Bayanin y ace dukkanin wadannan ‘yan jarida babu wani wanda ya aikata wani laifi, abin da ake tuhumarsu shi ne suna daukar rahotanni tare da yada labarai kan hare-haren da da jami’an tsaro suke kai wa kan falastinawa a cikin gaza da kuma sauran yankunan gabar yamma da kogin Jordan da Quds.

Yanzu ahka dai an yanke hukuncia kan 7 daga cikinsu, 4 kuma babu hukunci, 11 uma suna jiran hukunci.

 

3804420

 

captcha