Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, Cibiyar kula da kare hakkokin ‘yan jarida ta Falastinu ta fitar da wani bayani a jiya, wanda a cikinsa take bayyana cewa, a halin yanz akwai ‘yan jarida 22 a gidan kason Isra’ila da ake tsare da su 3 daga cikinsu mata ne.
Bayanin y ace dukkanin wadannan ‘yan jarida babu wani wanda ya aikata wani laifi, abin da ake tuhumarsu shi ne suna daukar rahotanni tare da yada labarai kan hare-haren da da jami’an tsaro suke kai wa kan falastinawa a cikin gaza da kuma sauran yankunan gabar yamma da kogin Jordan da Quds.
Yanzu ahka dai an yanke hukuncia kan 7 daga cikinsu, 4 kuma babu hukunci, 11 uma suna jiran hukunci.