IQNA

23:56 - May 03, 2019
Lambar Labari: 3483602
Bangaren kasa da kasa, an aike da wata wasikar barazana ga wani masallaci a birnin Berlin na kasar Jamus.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin ‘yan makonnin da suka gabata an aike da wasiku zuwa ga masallacin Gazi Osman Pasa da ke cikin Berlin na Jamus, inda ake yin barazana ga musulmi da suke yin salla a wurin.

Ali Senel limamin masallacin ya bayyana cewa, tun bayan kai harin kasar New Zealand, ake ta aiko da wasi na batunci ga barazana zuwa ga kwamitin masallacin, ya ce abin ya kara daga musu hankali shi ne, wasikar baya-bayan da aka tura musu tana dauke da harsashin bindiga.

Ya kara da cewa, tuni suka aike da wannan sako zuwa ga hukumar ‘yan sanda ta birnin Berlin, kuma suna fata  adauki matakan gaggawa kan lamarin, domin a wurin suke yin buda bakia  cikin azumi.

3808358

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Berlin ، Jamus ، gaggawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: