IQNA

23:59 - May 14, 2019
Lambar Labari: 3483640
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da ayyuka na fadada ayyukan kur'ani mai tsarkia kasar Uganda.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa,  an fara gudanar taruka na raya kur'an mai tsarki a kasar Uganda, wanda ake gudanarwa a masallatai da cibiyoyin addini a kampala da sauran biranan kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin ayyukan taruka na tilawar kur'ani, inda makaranta da maharda suke zuwa domin karatu, yayin da sauran jama'a musulmi suke sauarre.

Haka nan kuam akwai wuraren da ake gudanar tarukan da ake gudanar da tafsiri, inda malamai suke yin bayanai.

Daga cikin tarukan da za a gudanar a nan gaba a cikin wannan wata mai alfarma akwai haihuwar Imam Hassan (AS) da kuma shahadar Imam ali (AS).

Karamin ofishin jakadancin kasar Irana  kasar ta Uganda ne ke daukar nauyin wadannan taruka, tare da biyan malamai da makaranta da suke gabatar da tarukan.

3811484

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: