IQNA

22:28 - May 20, 2019
Lambar Labari: 3483657
Ministan harkokin wajen Iran ya mayarwa shugaban Amurka da martani dangane da barazanar da ya yi a kan akasar Iran.

kamfanin dilalncin labaran iqna, Zarif ya bayyana shafinsa na twitter cewa, yana kira ga Trump da ya daina yi wa Iran barazana:

Ya ce Trump ba zai iya yin abin da Iskandar da Chengiz suka kasa yi ba, Iran ba ta son shiga yaki da wata kasa, amma idan wata kasa ta tsokane ta, to ba za ta saurara mata.

Martanin na zuwa ne bayan wata barazana da Trump ya yi a jiya a kan shafinsa na twitter, inda yake da’awar cewa Amurka za ta kawo karshen kasar Iran baki daya, idan har yaki ya barke a tsakaninsu.

3813289

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Zarif ، Donald Trump ، barazana ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: