IQNA

21:12 - May 22, 2019
Lambar Labari: 3483664
Babban manzon majalisar dinkind uniya a kasar Libya ya yi gargadin cewa, ci gaba da rikcii a kasar Libya, ka iya kai kasar zuwa ga tarwatsewa baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Arab News ta bayar da rahoton cewa, a cikin rahoto da ya mika ga kwamitin tsaron majalisar dinkin kan halin da ake ciki a Libya, babban manzon musamman na majalisar dinkind uniya a kasar ta Libya Gassan Salamah ya bayyana cewa, halin da ake ciki a kasar Libya yana da matukar hadari.

Ya ce dole ne dukkanin bangarorin da suke aikewa bangarorin da suke rikici da makamai su dakatar, idan kuma ba haka ba, to kasar ta kama haryar wargajewa.

Tuna  ranar 4 ga watan Afirilun da ya gabata ne Khalifa Haftar ya fara kaddamar da hare-hare kan birnin Tripoli da nufin kwace iko da birnin, inda yake samun taimakon makudan kudade da makamai daga gwamnatocin Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa.

Bisa ga rahoton da hukumar lafiya ta duniya ta bayar, tun bayan da Haftar ya fara kaddamar da hare-hare kan birnin Tripoli, ya zuwa yanzu hakan ya yi sandadiyyar mutuwar daruruwan mutane, yayin da wasu fiye da dubu 75 suka tsere daga muhallansu.

3813925

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، muhallansu ، dubu ، halin da ake ، Libya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: