IQNA

23:54 - May 27, 2019
Lambar Labari: 3483678
Bangaren kasa da kasa, miliyoyin masoya ahlul bait ne suka taro jiya a hubbaren Imam Ali (AS) domin tunawa da zagayowar ranar shahadarsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na hubbaren Imam Ali (AS) cewa, a daren jiya miliyoyin masoyansa sun taru a hubbarensa da ke Najaf domin tunawa da zagayowar lokacin shahadarsa daga ciki da wajen kasar Iraki.

Mahalarta taron sun yi ta juyayin zagayowar wannan rana da kuma abin bakin cikin da ya faru a cikinta.

Masu gudanar da wakoki na makoki sun yi ta rera nasu baitocin na tunawa da wannan babban lamari da ya faru na shahadar shugaban limaman ahlul bait, Imam Ali (AS).

Kamfanin dillancin labaran Saumariyya News ya bayar da rahoton cewa, fiye da mutane miliyan 3 ne suka taru a hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf domin halartar wannan taro.

A daya bangaren kuma dubban jami’an tsaro ne aka girke domin bayar da kari da kuma tabbatar da tsaro a yayin gudanar da wadannan taruka a birnin na Najaf, yayin mutane kimanin 880 suka gudanar da ayyuka na hidima ga mahalarta taron.

3814999

تصاویری از بارگاه علوی در شب شهادت امام علی(ع)
 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: