IQNA

23:52 - May 28, 2019
Lambar Labari: 3483681
Wasu gungun mabiya addinin kirista sun halarci taron buda baki tare da musulmi a kasar Singapore.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jaridar Straits Times ta bayar da rahoton cewa, a jiya Litinin wasu gungun mabiya addinin kirista daga majami’ar The Church of Jesus Christ of Latter-Day Saints sun gudanar da buda baki tare da sauran musulmi a bababr cibiyar musulmi ta kasar Singapore.

Muhammad Hasbi shugaban cibiyar ya bayyana cewa, halartar mabiya addinin kirista a wurin buda baki tare da musulmi babban misali ne zaman lafiya da fahimtar juna da kyakkyawar alaka da ke tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista, wanda haka ya kamata ya zama tsakanin musulmi da kirista a duk inda suke a duniya.

Ko ranar Lahadin da ta gabata an gudanar da wani buda bakin makamancin wannan a bababr cibiyar taruka ta kasar, wanda ya samu halartar mutane kimanin 4000 da suka hada da musulmi da kirista, inda shugabar kasar ta Singapore ta zama babbar bakuwa a wajen taron buda bakin.

Adadin mutanen kasar ta Singapore dai ya kai miliyan 5.5, inda kashi 33 cikin dari mabiya addinin buda ne, 19 kuma mabiya addinin kirista, yayin da adadin musulmin kasar ya kai kashi 15 cikin dari.

3815150

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: