IQNA

Yau ce Ranar Shahadar Imam Sadeq (AS)

23:44 - June 29, 2019
Lambar Labari: 3483784
A yau ake juyayin zagayowar ranar shahadar Imam sadeq (as) a kasashen da daman a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, yau ce 25 ga watan shawwal na shekara ta dubu daya da dari hudu da arbain  wato ranar shahadar limami na 6 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (as) a Madina.

Imam Sadiq (as) ya yi zamani da wasu daga cikin sarakunan bani umayya, da kuma sarakuna na farko daga cikin sarakunan Abbasiyawa, sannan ya sami damar bude makaranta ko jami;a mafi girma a Madinan manzaon Allah (as) a zamanin, inda ya karantar da al-ummar musulmi fannonin ilmi masu yawa, daga cikin wadanda suka amfana da ilminsa akwai Maliku da Abu hanifa daga cikin limamai mazhabobin Ahlussuna.

Malaman tarihin sun bayyana cewa Imam Sadik (a) yanada dalibai kai tsaye ko kuma dalibansa kimani dubu hudu Kuma ana jingina Mazhabar iyalan gidan manzon Allah ta shia Itha’ashariyya a gare shi ne don kasancewa shi ne liamamin da ya sami damar yada ilmin iyalan gidan manzon Allah (s) mafi yawa idan an kwatanta da sauran limamain.

3822839

 

 

 

 

 

 

captcha