Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da suka ziyarci jakadan Iran a Ghana Ali Reza Faramarzi, tawagar gamayyar kungiyoyin musulmi a kasar ta nuna cikakken goyon bayanta ga Iran dangane da barazanar da Amurka ta yi wa kasar ta Iran tare da jadda goyon bayansu ga matsayin da Iran din ta dauka kan batun.
Hajji Abdul Mannan Abdulrahman shugaban gamayyar kungiyoyin musulmi a kasar ta Ghana ya bayyana cewa, abin da kasar Iran take fuskanta na matsin lamaba daga kasashe masu girman kai musamman Amurka, sakamako ne na tsayin dakan da take yi wajen kare martabar musulmia duniya.
Ya ce kasar ta Iran ita kadai ce a halin yanzu take fitar da muuslmi kunya a duniya, domin kuwa ba ta mika kai ga makiya addinin musulunc ba, kamar yadda kuma ba ta hada kai da su domina cutar da musulmi.
Daga karshe ya yi kira ga sauran kasashe da su koyi da hakan, matukar dai suna son su wanzu cikin daukaka ta addini.