IQNA

Zaman Taron Yaki Da Tsatsauran Ra’ayi A Mausel

23:58 - July 01, 2019
Lambar Labari: 3483798
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman karawa juna sani a garin Mausel na kasar Irakidomin yaki da yaduwar tsatasauran ra’ayi a tsakanin al’ummomin musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar kusanto mazhabobin musulunci cewa,a  jiya ne aka gudanar da zaman karawa juna sani a garin Mausel na kasar Irakidomin yaki da yaduwar tsatasauran ra’ayi a  tsakanin al’ummomin musulmi musamman matasa.

Shugaban jami’ar Mausel Qosei Al-Ahmadi shi ne ya bude taron da jawabinsa na farko dangane matsayin addini kan akidar kafrta muuslmi da kuma iin mummunan tasirinta a cikin musulmi

A cikin bayanin nasa ya bayyana wannan akida da cewa ba ta da wata alaka da muslunci, kuma wadanda suke dauke da irin wannan akida wada ita ce hakikanin akidar ‘yan ta’adda, ba ta da dangantaka da musulunci.

Shi ma anasa bangare Jair Aljabiri wakilin maa’ikatar bude ido ta kasar Iraki, ya bayyana cewa yaduwar akidar kafirta musulmi ta yi babban tasiri wajen ruda matasa wadanda ake yaudara suna shiga ayyukan ta’’addaci da sunan jihadi.

Baya ga musulmi da suka halrci wurin, an kuma gayyac wasu daga cikin malaman addinain kirista na kasar ta Iraki, wadanda wasu daga cikinsu suka gabatar da nasu kasidun.

Matran Sabet Habib daya daga cikin malaman addinin kirista da suka halarci wurin ya bayyana cewa, babu wani addini da aka saukar daga sama da ya zo da ta’addani ko kian bil adama ba tare da dalili ba, a kan haka idan aka ga wani muuslmi ko kirista yana aikata haka bay a wakiltar addininsa.

 

3823474

 

 

captcha