IQNA

22:46 - July 13, 2019
Lambar Labari: 3483834
Bangaren kasa da kasa, a jiya ne aka bude bababn masallacin Azahar da ke cikin babban ginin cibiyar a birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran qina, an bude bababn masallacin Azahar da ke cikin babban ginin cibiyar a birnin Alkahira tare da halartar manyan malamai da kuma jami’an gwamnati.

Abdulmun’im Fuad shi ne shugaban kwamitin masallacin, ya gabatar da jawabi, inda ya yaba da irin himmar da aka nuna wajen aikin ginin masallacin.

Ya ce dukkanin bangarori sun yi kokari, kama daga bangaren mahaukuntan cibiyar ta Azhar, da kuma bangaren gwamnati gami da malamai da kuma daidakun mtane da suka taimaka wajen ganin wannn aiki ya kammala.

Cibiyar azhar dai it ace cibiyar ilimi mafi girma ta malaman sunna a duniya, wadda ta yaye dubban daruruwan dalibai daga sasa na duniya, kamar yadda kuma take ci gaba da gudanar da ayyuka a dukkanin bangarori na ilimi.

 

 

3826522

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: