IQNA

22:58 - July 27, 2019
Lambar Labari: 3483887
Bnagaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Bahrain ta zartar da hukuncin kisa akan wasu matasa masu fafutuka sabosa ra'ayoyinsu na siyasa.

Gwamnatin kasar Bahrain ta zartar da hukuncin kisa kan yan kasar guda 3 kan laifuffuka da suka shafi ayyukan ta’addanci da kuma kashe wani jami’in tsaro, inji wata majiyar shari’a a kasar.

Mutanen da aka zartarwa hukuncin kissan dai sun hada da Ahmad Al-Mullali dan shekara 24 da Ali Hakim Al-Arab dan shekara 25.

Kafin haka dai, a shekarar da ta gabata ce, wata kotu a kasar ta Bahrai ta yanke hukuncin kisa kan wadannan mutane, tare da wasu mutane hamsin da shida.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da dama sun yi kira ga gwamnatin Bahrain ta dakatar da hukuncin kisa kan wadannan matasa amma bata sauraresu ba.

Labarin ya kara da cewa an zartar da hukuncin kisan kan yan kasar ta Bahrain ne bayan ganawarsu ta karshe da iyayensu da kuma danginsu a kurkukun Jaw da ke birnin Manama babban birnin kasar.

3830126

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، hukuncin kotu ، bahrain ، kisa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: