IQNA

22:26 - August 13, 2019
Lambar Labari: 3483943
Bangaren kasa da kasa, sheikh Ibrahim Zakzaky ya isa kasar India domin neman magani a asibiti.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaban Harka Islamiyya a tarayyar Najeriya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya isa birnin New Delhi na kasar Indiya inda zai fara jiyar rashin lafiya da yake fama da ita tun bayan harin da sojoji suka kai wa gidansa a shekara ta dubu biyu da sha biyar.
 
Tashar talabijin ta Channeltv a Najeriya ta bayyana cewa shehinmalamin tare da matarsa da kuma wadanda suke yi masa rakiya daga cikin danginsa da kuma jami’an tsaron Najeriya sun isa kasar Indiya a yau Talata da misalin karfe biyu an rana, bayan sun yada zango a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa UAE.
 
Ana sa-ran likitoci a asbitin Medanta dake kilomita 30 daga wajen birnin New Delhi zasu kula da lafiyarsa, daga cikin matsalolin da yake fama da su kuwa akwai matsalar wuya, gurbatar jininsa da sinadarai masu guba, da kuma cire albarusai da sauransu daga jikinsa.
 
A ranar Litinin ta makon jiya ce wata kotu a birnin Kaduna ta amincewa sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya nemi lafiyarsa a kasar India amma tare da rakiyar jami’an tsaron Nigeriya domin tabbata da cewa ya dawo gida bayan sallamarsa daga asbiti.
 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، zasu ، kula ، Zakzaky ، India
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: