IQNA

22:34 - August 26, 2019
Lambar Labari: 3483989
Bangaren kasa da kasa,  dakaruun Ansarullah na kasar Yemen sun harba jirgin yaki marassa matuki samfurin Sammad zuwa tungar makiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Almasirah ta bayar da rahoton cewa, da safiyar yau dakarun kasar  Yemen sun kaddamar gagarumin  hari na mayar da martani a kan wasu muhimman wurare na sojin masarautar Al saud da ke kusa da Yemen da ma wadanda ke nesa..

Kakakin rundunar sojin kasar Yeman Brigadier Janar Yahya Sari daga birnin San’a ya bayyana cewa, dakarun kasar sun kaddamar da wani gagarumin harin ramuwar gayya a kan wasu muhimman wurare na soji na makiya al’ummar yemen.

Haka nan kuma ya ce sun harba makamai masu linzami guda goma a lokaci guda kuma duk sun sauka inda a ke bukata a kan filin sauka da tashin jiragen sama na Jizan da ke kudancin saudiyya..

Bayan nan kuma dakarun na Yemen sun harba wasu makaman ta hanyar yin amfani da jirgin sama maras matuki samfurin sammad, wanda shi ma ya kai nasa hare-haren a kan filin sauka da tashin jiragen sama na sarki Khalid da ke kusa da birnin Riyad.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar ta Yemen ya ce dukkanin wadannan hare-hare suna zuwa ne a matsayin na daukar fansa, kan hare-haren kisan kiyashi da masarautar Al saud take kaddamarwa  akan al’ummar kasar Yemen.

Ko a  cikin wanann mako sun kashe fararen hula masu yawa a yankuna daban-daban na kasar ta Yemen tare da jikkata wasu.

3837699

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Al saud ، kaddamarwa ، Yemen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: