IQNA

Micheil Aoun: Shigar Jiragen Yakin Isra’ila Lebanon Shelanta Yaki Ne

22:36 - August 26, 2019
Lambar Labari: 3483990
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Lebanon Micheil Aoun ya bayyana kutsen da jiragen yakin Isra’ila suka yi a Lebanon da cewa shelanta yaki ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin jaridar alahd ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Labanon Michel Aoun ya yi tir da harin wuce gona da iri da jiragen yakin Isra'ila suka kai kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar, inda ya ce wannan alama ce ta takalar fada.

A safiyar yau Lahadi ne kafafen yada labarai suka bayar da rahotannin kakkabo jiragen yakin Isra'ila biyu marassa matuki a yankin kuduncin birnin Beirut bayan wani yunkurin kai hari da suka yi wanda ci nasara ba.

Shugaban kasar Labnon Michel Aoun yayin da yake mayar da martani kan harin na haramtaciyar kasar Isra'ila na cewa; wannan wani sabon makirci ne da nufin yamutsa zaman lafiyar kasar Labnon da ma yankin baki daya.

A nata bangare, Ministar cikin gidan kasar ta Labnon ta ce wannan hari ya karya hurumin kasar Labnon kuma ya karya doka mai lamba dubu da dari bakawai da daya, ta Majalisar Dinkin Duniya.

Shi kuma Ministan harakokin wajen kasar ta Labnon ya ce kasarsa za ta kai karar haramtaciyar kasar Isra'ila gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan yadda take keta hurumin kasar.

Shugaban Majalisar koli ta mabiyar mazhanar Shi'a a kasar ta Labnon da Sa'ad Hariri Firayi ministan kasar, dukkaninsu sun yi tir da harin na Isra'ila tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin kasar ta Labnon.

3837747

 

 

captcha