IQNA

Hizbullah ta Kakkabo Jirgin leken Asirin Isra’ila

17:42 - September 09, 2019
Lambar Labari: 3484034
Hizbullah ta Kakkabo Jirgin leken Asirin Isra’ila
Bangaren kasa da kasa, Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun harbo jirgin yaki maras matuki na Isra’ila.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, shafin yada labarai al-ahad ya bayar da rahoton cewa, a wata sanarwa da kungiyar gwagwarmayar musuluncin ta Hizbullah ta fitar dazu, ta ce; An yi amfani da makamin da ya dace wajen harbo jirgin saman maras matuki na Isra’ila a garin “Ramiyah”

Sanarwar ta ci gaba da cewa; Bayan harbo jirgin saman maras matuki, ‘yan gwagwarmayar sun dauke shi yana hannunsu.

Tun bayan harin da Isra’ila ta kai da jirgi sama maras matuki a unguwar Dhahiya dake cikin birnin Beirut, babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sayyid Nasarllah ya bayyana cewa; Daga yanzu kungiyar za ta rika harbo jiragen sama maras matuki na Isra’ila.

3841136

 

captcha