IQNA

23:00 - September 25, 2019
Lambar Labari: 3484087
Bangaren kasa da kasa, an kame mutane sama da 650 a zanga-zangar nuna kiyayya ga shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, wasu rahotannin sun ce sama da mutane dubu daya ne aka kame bayan zanga-zangar neman Shugaban kasar Masar ya yi murabus

Cikin wata sanarwa da kungiyoyin fara hula suka sanar a wannan laraba, jami'an tsaron kasar Masar sun kame mutane sama da dubu daya a yayin zanga-zangar kijin gwamnati da kuma neman shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya yi murabus daga kan mukaminsa a makon da ya gabata.

A ranaikun juma'a da Asabar din da suka gabata ce al'ummar kasar Masar suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a Alkahira da wasu manyan biranan kasar na neman shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya yi murabus daga kan mukaminsa, inda aka kame sama da mahalarta zanga-zangar dubu daya da suka hada da 'yan jarida da kuma 'yan siyasa.

Sanarwar da gamayar kungiyoyin farar hula na kasar Masar din suka fitar sun ce daga ranar 20 ga watan satumba zuwa yanzu an kame mutane sama da dubu daya a kasar, kuma daga cikin wadanda aka kama akwai daliban jami'a da shahararun 'yan siyasa da masu fafutukar kare hakin bil-adama a kasar.

3844220

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، El sisi ، zanga-zanga ، masar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: