IQNA

23:50 - September 29, 2019
Lambar Labari: 3484099
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taro mai taken Asura a yaua  kasar Jamus.

Kamfanin dillancin labaran iqna daga kasar Jamus ya bayar da rahoton cewa,a  yau an gudanar da taro mai taken Asura a Jamus tare da halartar matasa musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, domin yi musu bayani kan hakikanin ranar Ashura da kuma abin da ya faru da Imam Hussain (AS).

Hojjatol Islam Muhammad Razavidar ne ya gabatar da jawabia  wurin, inda aka tabo muhimman lamurra da suka wakana kan zuriyar manzon Allah tsira da amincin Alah su tabbata a gare shi a wannan rana.

Babbar manufar taron dai ita ce wayar da kai ga matasa wadanda basu da masanya kan hakikanin abin da ya faru a tarihin musulunci a wannan rana, wanda wasu suna bukatar sanin hakan amma babu inda za su samu bayani na hakika.

3845693

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، imam hussain ، jamus ، ashura
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: