IQNA

23:55 - October 06, 2019
Lambar Labari: 3484126
Bangaren kasa da kasa, hare-haren kungiyar Boko Haram sun ci rayukan mutane 16 a cikin jihar Borno.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoly cewa, ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hare-hare a  kauyen Maru da ke cikin jihar Bornon a arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.

Bayanin farko dai an tabbatar da mutuwar mutan 16 da suka hada da sojoji 11 daga cikinsu, amma rahotanni sun ce adadin zai iya haura.

Wasu rahotannin da ska zo daga bisani sun mutane ashirin da bakawai ne suka mutu sakamakon hare-haren na Boko Haram, kuma mafi yawan wadanda suka mutu jami’an tsaro ne.

Koa  cikin makon da ya gabata ‘yan ta’addan sun kaddamar da wasu hare-haren a kan wasu cibiyoyin jami’an tsaro guda a cikin jihar ta Borno.

Kungiyar Boko Haram da ke da akidar kafirta musulmi ta fara gudanar da aikace-aikacenta ne daga cikin jihar ta Borno fiye da shekaru goma da suka gabata, inda daga bisani ta zama karfen kafa ta fuskar tsaro a kasar.

3847618

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، tsaro ، karfen kafa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: