IQNA

23:49 - October 26, 2019
Lambar Labari: 3484193
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Ukraine na shirin bude wani ofishin wakilci a birnin Quds da ke karkashin mamayar yahudawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Ukraine ta bayar da sanarwar cewa, tana shirin saka gudanar da wasu ayyuka na saka hannayen jari a Isra’ila, a kan haka za ta bude ofishin wakilci a birnin Quds, wanda zai zama a a matsayin karamin  ofishin jakadancinta.

Bayanin ya ce baya ga birnin na Quds za a bude wasu ofisoshin na wakilci a wasu garuruwan da za su zama karkashin kulawar ofishin na birnin Quds.

Yesrael Katz ministan harkokin wajen Isra’ila ya yi lale marhabin da matakin na gwamnatin Ukraine.

A cikin wanann shekara da muke ciki daruruwan yahudawa ne suka yi hijira daga Ukraine zuwa Isra’ila, inda aka tsugunnar da su a matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna da ke kusa da yankin zirin Gaza.

 

3852534

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: