IQNA

Gargadi Kan Bullar Boko Haram A Sudan

23:16 - October 28, 2019
Lambar Labari: 3484201
Kawancen jam’iyyu da kungiyoyin Canji a Sudan ya yi gargadi kan yiwuwar bullar Boko Haram a Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Ismat Muhammad daya daga cikin jagororin kawacen jam’iyyu da kungiyoyin Canji a Sudan ya bayyana cewa, sun yi gargadi kan yiwuwar bullar Boko Haram a kasar.

Ya ce dole ne jami’an gwamnati da jami’an tsaro su zama cikin fadaka dangane da barazanar wadannan ‘yan ta’adda, domin kuwa kasar tana kusa da yankunan da suke aikata ayyukansu na ta’adanci.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai mutane masu ra’ayoyi daban-daban, kuma akwai mas tsatsauran ra’ayin addini da tuanninsu ya yi kama da na irin wadannan ‘yan ta’adda, wadanda suke saurin kafirta muuslmi da kirans mushrikai kana bin da bai taka kara ya karya ba, wanda a cewarsa hakan babban hatsari ne ga makomar kasar.

Kungiyar Boko Haram dai ta fara ayyukanta ne daga Najeriya, kafin daga bisani ta bazu zuwa kasashe makwata, musamman Nijar, Kamaru da kuma Chadi da ke makwataka da kasar ta Sudan.

 

3852966

 

 

captcha