IQNA

Macron Ya Yi Allawadai da harin Da Aka Kai Kan Mallaci A Faransa

22:57 - October 29, 2019
Lambar Labari: 3484202
Shugaban kasar Faransa ya yi Allawadai da harin da aka kai kan wani masallaci a kasar Farasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macro ya yi Allawadai da harin da aka kai kan wani masallaci a garin Bayonne da ke kudu maso yammacin kasar.

Macron ya ce abin da ya faru na kai hari a kan masallacin musulmi abin yin tir da Allawadai ne, kuma ba abu ne da za a lamunta da shi a kasar ba.

Jami’an ‘yan sandan kasar Faransa sun ce sun kame mutumin da ya kai arin, wanda tsohon dan takarar kujerar majalisar dokokin kasar ne daga jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya.

A yayin kai harin dai mutane biyu da suke fitowa daga cikin masallacin kai harin sun samu raunuka, bayan da mutumin ya bude wuta kan mai uwa da wabi a kan masallacin.

 

3853210

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Macron ، Faransa ، Bayanne ، masallaci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha