IQNA

21:43 - November 02, 2019
Lambar Labari: 3484216

Jiragen Yakin Isra'ila Sun Kai Hari A Gaza

Bangaren kasa da kasa, sojojin Isra'ila sun kai hari a Zirin Gaza inda suka kashe bafalastine guda da jikkata wasu.

Jiragen Yakin Isra'ila Sun Kai Hari A Gaza

Rahotanni da ke fitowa daga yankin palasdinu sun bayyana cewa jiragen yakin Isra'ila sun yi lugudan wutakan wasu wuraren kungiyar gwagwarmaya ta hamas aKhan yunusda wasu yankuna a zirin gaza kuma yayi sanadiyar shahadar mutum daya, sao’ibayan da sojojin Isra'ila sun jikkata gomomin palasdinawa a lokacin da suke gudanar da zanga zanga a yakin gabar teku .

Kamfanin dillancin labaran iqna, wata sanarwa da jami’an soji Isra'ila suka fitar sun nuna cewa harin na jiya sun kai shi ne a matsayin mayar da martani game da makaman roka 10 da aka harba su zuwa Israila daga yankin zirin gaza

A gafe guda ma sojojin Isra'ila sun bude wuta kan wasu palasdinawa masunta a Arewacin yankin Gaza, bayan jikkata palasdinawa da dama a ya yin gudanar da zanga zangar neman hakkin palasdinawa yan gudun hijira su koma gida.

A wani rahoto da ma’aikatar kiwon lafiya ta Yankin Gaza ta fitar ya nuna cewa: wani bapalasdine guda ne ya yi shahada ya yin da wasu casain da shida kuma suka samu raunuka sakamakon taho mu gaba da aka yi da sojojin Isra'ila a ya yin zanga –zangar ta jiya juma’a.

3853888

 

 

captcha