IQNA

Hatami Iran Ta Samu Ci Gaba A Bangaren Tsaro

18:28 - November 12, 2019
Lambar Labari: 3484243
Ministan tsaron Iran Janar Hatami ya bayyana cewa, kasar ta yi nisa matuka wajen bunkasa ayyukan kere-kere ta fuskar tsaro.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a jiya a birnin Tehran, ministan tsaron kasar Iran Janar Amir Hatami ya bayyana cewa; duk da irin matsin lamba da Iran take fuskanta daga kasashe masu girman kai, amma hakan ba iya hana ta ci gaba da inganta kere-kerentaa bangaren tsaro ba.

Ya ce a halin yanzu kasar ta dogara da kanta wajen ayyukan kera makamai, da dukkanin sauran kayayyakin da take bukata domin gudanar da ayyukan tsaro, da hakan ya hada da jiragen yaki marassa matuki na zami wadanda take samarwa.

Haka nan kuma ya bayyana cewa; wannan shi ne babba abin da zai baiwa kasar kariya da kuma tabbatar mata da tsaro, kamar yadda kuma har kullum take fatan ganin kasashen yankin sun fahimci cewa dogaro da kai da kuma yin aiki tare tsakanin dukkanin kasashen yankin shi ne mafita a gare su, ba dogaro da kasashen yammacin duniya ba.

3856270

 

captcha