IQNA

15:08 - December 05, 2019
Lambar Labari: 3484294

Masar Ta Yi Gargadi Kan Yin Amfani Da Kalmar Ta’addancin Musulunci

Bangaren kasa da kasa, cibiyar bayar da fatawa a Masar ta yi gargadi kan yin amfani da Kalmar ta’addancin musulunci.

Masar Ta Yi Gargadi Kan Yin Amfani Da Kalmar Ta’addancin Musulunci

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin tashar Russia Today ya bayar da rahoton cewa, a jiya babbar cibiyar bayar da fatawa a Masar ta yi gargadi kan yin amfani da Kalmar ta’addancin musulunci tare da bayyana hakan a matsayin wata hanya ta bakanta fuskar musulunci, da aka fara amfani da ita a 2001.

Cibiyar ta ce babu wani abu ta’addancin musuluci domin kuwa addinin musulunci ba addinin ta’addanci ba ne, saboda haka ba abu ne da za a amince da shi ba a ci gab ada yin amfani da wannan kalma dake danganta ayyukan ta’addanci da musulunci.

Darul Ifta Masar ta ce bayan kai harin 11 Satumba a 2001 ne aka fara yin amfani da Kalmar, sai kuma a harin Madrid 2004, da London 200, da Stockholm 2010, da kuma bayan kirkiro Daesh a 2014.

 

3861865

 

https://iqna.ir/fa/news/3861865

captcha