IQNA

22:36 - December 08, 2019
Lambar Labari: 3484302
Bangaren kasa da kasa, masanin nan dan kasar Iran ya iso gida tsare shi a kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Soleimani ya iso filin jirgin saman Mehrabad da ke birnin Tehran tare da ministan harkokin wajen Iran din bayan an sako shi daga Amurka sakamakon wani musayen fursunoni da aka cimma tsakanin Iran da Amurkana birnin Zurich na kasar Switzerland.

A wata tattaunawa da yayi da manema labarai jjim kadan bayan isowarsa Tehran din, Dr. Soleimani ya ce irin nasarorin da Iran take samu a fagen ilimin kimiyya da fasaha na daga cikin abubuwan da suke sanya Amurka fushi da kuma gaba da Iran, yana mai kiran masanan Iran da su ci gaba da kokarin da suke yi wajen ciyar da kasar gaba kamar yadda kuma ya gode wa jami’an Iran saboda kokarin da suka yi wajen sanya a sako shi daga Amurkan.

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen na Iran ya jami’an tsaron Amurka ne sun kama Dr. Soleimani da ci gaba da tsare shi na sama da watanni 14 ba tare da wani dalili ba, yana mai cewa a lokuta da dama jami’an Amurka sun yi wa Dr. Soleimanin tayin zama a Amurka ba tare da ya dawo Iran ba amma masanin ya ki amincewa sakamakon kishin kasarsa.

An sako Dr. Soleimanin ne dai bayan wani musayen fursunoni da ya gudana tsakanin Iran da Amurka, inda Iran din ta sake wani Ba’amurke dan asalin kasar China Xiyue Wang wanda aka kama da kuma yanke masa hukuncin zaman gidan maza na shekaru 10 sakamakonsa samunsa da laifin leken asiri da aka yi.

 

3862324

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، Amurka ، masani
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: