IQNA

23:41 - January 24, 2020
1
Lambar Labari: 3484446
Yahudawan Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan masalata a cikin masallacin Quds tare da kame falastinawa 13.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, wasu kafafen yada labarai na Palasdinawa sun bada labarin cewa sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila  sun farwa palasdinawa a masallacin Qudus a safiyar yau jumma’a don hanasu sallar jumma’a a cikin masallacin mai alfarma.

Rahotanni sun bayyana cewa, yahudawa sun yi harbi da harsashi na roba, sannan sun auka wa wasu palasdianwan da duka sannan suka kame wasu suka tafi da su wani wuri da ba a sani ba.

Haka nan kuma a yau a garin Bait Safafa kuma, wanda yake kusa da birnin Qudus, yahudawan sun kona wani masallaci, amma tare da taimakon wasu palasdinawa a garin massalacin bai kone duka ba.

Wadannan matakai an tsokana na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin yahudawa take kara fuskanatar matsin lamba a cikin gida, wanda hakan ke nufin dauke hankulan sauran yahudawa daga matsalolinsu.

 

https://iqna.ir/fa/news/3873774

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Sambo saidu
0
0
Allah kawo karshensa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: