IQNA

Husni Mubarak Na Masar Ya Rasu

23:03 - February 25, 2020
Lambar Labari: 3484558
Tsohon shugaban kasar Masar Husni ya rasu a yau Talata bayan fama da rashin lafiya dogon lokaci

Kafar labarai ta kasar Masar Alyaum Sabi ta bayar da rahoton mutuwar Husni Mubarak a rahotanninsu na yau Talata.

Babban dansa Ala Mubarak ya sanar da cewa an yi wa mahaifinsa aikin tiyata a daya daga cikin asibitocin birnin Alkahira tun a cikin watan Janairu.

Haka nan kuma Ala ya bayyana cewa, mahaifinsa yana kwance a dakin kulawa ta musamman tun bayan yi masa aikin tiyataa  asibiti.

3881410

 

captcha