IQNA

23:43 - March 27, 2020
Lambar Labari: 3484662
Tehran (IQNA) Sakamakon gwaji ya tabbar da cewa Boris Johnson ya kamu da corona.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya habarta cewa, a cikin wani sako na twitter, firayi ministan kasar Burtaniya a sanar da cewa ya kamu da corona.

A cikin wani bayani da ya dauka da bidiyo, Johnson ya bayyana cewa, ya fara ganin alamun kamuwa da cutar corona a jikinsa, a kan haka aka yi masa gwaji, kuma sakamakon ya tabbatar da hakan.

Boros Johnson ya cea  halin yanzu ya killace kansa, kuma daga gida ne yake tafiyar da ayyukan gwamnatinsa.

Baya haka ma kafofin yada labarai na kasar Burtaniya sun habarta cewa, ministan kiwon lafiya na kasar shi ma ya kamu da cutar da corona.

 

 

3887690

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: