IQNA

23:39 - April 02, 2020
Lambar Labari: 3484677

An Hana Kai Komo A Biranan Makka Da Madina

Tehran (IQNA) mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da hana duk wani kai komo a cikin biranan Makka da Madina har sai abin da hali ya yi.

An Hana Kai Komo A Biranan Makka Da Madina

Kamfanin dillancin labaran Saumaria Nws ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, daga yau 2 ga watan Afirilu an kafa dokar hana fita da kai komo a cikin biranan Makka da Madina.

Sanarwar ta ce an dauki wannan mataki ne da nufin daikile yaduwar cutar corona a cikin kasar, kasantuwar wadannan birane biyu nan ne aka fi gudanar da harkoki wasu tara jama’a.

Wannan doka ta shafi ‘yan kasa da ma baki ‘yan kasashen ketare da suke a cikin kasar a halin yanzu, duk da cewa akwai ma’aikata a wasu bangarori da dokar ba ta shafe su ba, kamar jami’an tsaro, da ma’akatan kiwon lafiya da sauransu.

Tun a cikin makon da ya gabata ne dai sarkin masarautar Saudiyya ya bayar da umarnin daukar kwararan matakai na dakile yaduwar corona a kasar, musamman a biranan Riyad, Makka da kuma Madina.

3888702

 

 

 

 

captcha