IQNA

Shugaban Iraki Ya Umarci Kazemi Da Ya Kafa Gwamnati

23:36 - April 09, 2020
Lambar Labari: 3484696
Tehran (IQNA)  shugaban Iraki ya sanar da nada Moustafa al-Kazimi domin kafa gwamnati bayan da wanda ya gabace shi, Adnane Zorfi, ya yi watsi da kafa gwamnatin.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, Musatafa Kazemi wanda shi ne shugaban hukumar leken asirin kasar ta Iraki, kafin shugaban kasar ya ba shi wannan damar kafa gwamnati, ya karbi umarni domin kafa sabuwar majalisar ministoci.

Ana dai kallonsa a matsayin mutuman dake samun goyan bayan kusan illahirin bangarorin siyasar kasar ta Iraki.

Baya ga hakan kuma ana kallonsa a matsayin wanda ke samun goyan bayan Amurka, kafin ya fara farfado da dangantakarsa da mahukuntan Teheran.

Hakazalika Kazimi, babban amini ne ga yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed Ben Salmane, wanda kuma hakan zai bashi damar lalubo bakin zaren matsalolin da kasar ta Iraki ke fama dasu.

Daga cikinsu akwai samar wa da kasarsa sassaucin takunkuman Amurka domin ci gaba da hulda da Iran musamman ta bangaren wutar lantarki da kasarsa ke da matukar bukata daga Iran.

 

3890474

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki shugaban kasa gabace gwamnati kafa watsi
captcha