IQNA

An Janye Gudanar Da Tarukan Idi Mai Tsarki A Quds

23:40 - April 10, 2020
Lambar Labari: 3484698
Tehran (IQNA) a karon farko a cikin shekaru 100 an sanar da janye gudanar da tarukan idi mai tsarki da ake gudanarwa a babbar majami’ar kiyama da ke Quds.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, majami’ar kiyama ta mabiya adinin kirista da ke birnin Quds, ta sanar da cewa a wannan karon an janye gudanar da tarukan da aka saba gudanarwa a kowace shekara na idi mai tsarki.

Bayanin ya ce a wannan shekara mutane 6 ne kawai za su halarci taron, wanda kuma za a saka a shafukan yanar gizo da kuma gidajen talabijin kai tsaye.

Daga cikin wadanda za su halarta akwai manyan malaman darikar Katolika daga birnin Rom, da kuma Protestant, wanda suke gudanarwa a ranar Asabar 12 ga Afirilu, sai kuma wakilan majami’ar Arthodox wadanda su kuma suna gudanar da nasu taron ne a ranar 19 ga watan Afirulu.

Mabiya addinin kirista sun yi iamnin cewa a irin wannan rana ce bayan an cire gawar annbi Isa daga sakandami, ya sake dawowa a raye.

 

3890588

 

 

 

 

captcha